Gwamnatin Amurka ta ware kusan Naira biliyan 587 domin ayyukan yaki da ta’addanci a Nijeriya da wasu kasashen Afirka a shekarar 2026, sakamakon tabarbarewar tsaro a yankin Yammacin Afirka.
Kudaden suna cikin Dokar Kasafin Tsaron Amurka ta 2026 (NDAA), wadda ta amince da kashe dala miliyan 413.046 ga rundunar sojin Amurka a Afrika (AFRICOM), kamar yadda takardun da aka samu suka nuna. Dokar ta samu sahalewar Shugaban Amurka, Donald Trump, a ranar 18 ga Disamba, 2025.
Kasafin ya zo ne a lokacin da Nijeriya ke fama da ta’addanci a Arewa maso Gabas, fashin daji a Arewa maso Yamma, da kuma laifukan teku a Tekun Guinea, yayin da kasashen Mali da Benin ke fama da hare-haren ‘yan jihadi daga yankin Sahel.
Dokar ta kuma tanadi kafa ofishin Mataimakin Sakataren Harkokin Afirka a Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka, domin sa ido da daidaita manufofin Amurka a Afirka ta Kudu da Sahara, tare da bibiyar tasirin dabarun soja na Rasha a nahiyar.



