Mataimakin Shugaban Nijeriya, Kashim Shettima, ya tashi daga Abuja domin wakiltar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a bikin rantsar da sabon shugaban ƙasar Guinea-Conakry, Mamadi Doumbouya. Bayan wannan, zai halarci taron shekara-shekara na World Economic Forum (WEF 2026) a Davos, Switzerland, daga 19 zuwa 23 ga Janairu.
Shugaba Doumbouya zai karbi rantsuwa a GLC Stadium, Nongo, a ranar Asabar, 17 ga Janairu. Halartar Shettima yana da nufin ƙarfafa jagorancin Najeriya a ECOWAS, tallafawa dawowar Guinea ga tsarin mulki, da kuma zurfafa hulɗar tattalin arziki tsakanin ƙasashen biyu.
A baya-bayan nan, fitar da kayayyakin Najeriya zuwa Guinea, musamman kayan masana’antu da noma, ya kai dala miliyan 3.29.
Bayan Guinea, Mataimakin Shugaban Nijeriya zai shiga WEF 2026 a Davos, inda shugabanni daga gwamnatoci, kasuwanni, ƙungiyoyi, da masana kimiyya za su tattauna kan ci gaban fasahar zamani kamar AI, quantum computing, biotechnology, da makamantansu. Taron zai mayar da hankali ne kan yadda za a yi amfani da waɗannan fasahohi don haɓaka tattalin arziki, samar da damar aiki, da ci gaba mai ɗorewa.
Shettima zai yi amfani da damar wajen tattaunawa da shugabanni da masu zuba jari kan tsare-tsaren gyaran tattalin arziki na Nijeriya, damar zuba jari, da rawar da Afirka ke takawa wajen ƙirƙirar makoma mai ɗorewa. Ana sa ran zai dawo Najeriya bayan kammala ayyukansa a Davos.



