Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma na Nijeriya, Alhaji Mohammed Idris, ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu na shimfiɗa tubali mai ƙarfi domin bunƙasar tattalin arziki na dogon lokaci da walwalar al’umma baki ɗaya.
Ministan ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi mambobin ƙungiyar Grassroots Advocacy for Tinubu (GAT) 2027 da suka kai masa ziyarar ban girma a Abuja, kamar yadda wata sanarwa daga Mataimaki na Musamman kan Harkokin Watsa Labarai, Malam Rabiu Ibrahim, ta nuna.
Alhaji Mohammed Idris ya ce gwamnatin Tinubu ta ɗauki matakai masu tsauri, wasu ma masu wahala, domin daidaita harkokin ƙasa da sanya Nijeriya kan hanya mai ɗorewa ta fuskar tattalin arziki.
Ya ƙara da cewa duk da ƙalubalen da ake fuskanta, alamu na fara bayyana na farfaɗowar tattalin arziki a muhimman fannoni, yana mai jaddada cewa manufofin gwamnatin na nufin samar da ci gaba mai dorewa da romon dimokuraɗiyya ga ’yan Nijeriya gaba ɗaya.


