Dattawan al’ummar Gidan Waya da ke ƙaramar hukumar Lere a jihar Kaduna sun bayyana cewa sun sayar da buhunan masara sama da 3,000 domin tara Naira miliyan 40 da masu garkuwa da mutane suka nema a matsayin kudin fansa, amma duk da biyan kudin, mutane 13 da aka sace har yanzu na ci gaba da zama a hannun masu garkuwa bayan shafe makonni.
Da yake magana a wani taron manema labarai da aka gudanar a Kaduna ranar Litinin, Shugaban Kwamitin Dattawa, Malam Rabo Sambo, ya bayyana cewa ‘yan bindiga sun kai hari al’ummar Gidan Waya ne da tsakar dare a ranar 11 ga Nuwamba, 2025, inda suka kashe mutane hudu, sannan suka yi garkuwa da mutane 13 da suka hada da maza biyar da mata takwas.



