Rundunar sojin Najeriya ta amince cewa wasu jami’anta sun kitsa yunkurin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
A watan Oktoban shekarar da ta gabata ne rahotanni suka bayyana cewa an kama tare da tsare wasu jami’an soja, daga mukamin Kyaftin har zuwa Birgediya Janar, bisa zargin shirya juyin mulki.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Hukumar Leken Asiri (DIA) ce ta gudanar da kamen.
A wancan lokaci, Hedikwatar Tsaro da kuma Fadar Shugaban Ƙasa sun musanta cewa akwai yunkurin juyin mulki, duk da rahotannin da suka danganta lamarin da soke bikin faretin Ranar ‘Yancin Kai ta 1 ga Oktoba da Shugaba Tinubu ya yi.
Sai dai a wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labaran Tsaro, Manjo Janar Samaila Uba, ya fitar, ya tabbatar da cewa kwamitin binciken da aka kafa ya kammala aikinsa tare da miƙa rahoton ga “hukumomin da suka dace”.
Uba ya ce duk jami’an da ake tuhuma, za a gurfanar da su a gaban kotun soja da ta dace, domin fuskantar shari’a bisa tanadin Dokar Rundunar Sojoji da sauran ƙa’idojin aiki da suka dace.



