An kai hari ga ‘yar Majalisar Wakilan Amurka, Ilhan Omar, inda wani mutum ya nemi caka mata allura yayin taron jin tattaunawa da jama’a da ta gudanar a birnin Minneapolis, jihar Minnesota.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a lokacin da Ilhan Omar, wadda ke wakiltar jihar Minnesota a Majalisar Wakilan Amurka, ke tattaunawa da jama’a.
Jami’an tsaro sun tabbatar da cewa an kama wanda ake zargi nan take a wajen taron.



