Gwamnatin Jihar Kano ta tabbatar da cewa rikicin da ya dabaibaye batun masarautu a jihar zai samu waraka cikin lumana nan ba da jimawa ba.
Kwamishinan yaɗa labarai da Harkokin cikin gida Ibrahim Waiya ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a Kano, inda ya ce gwamnati ta ɗauki matakai masu ƙarfi domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali mai ɗorewa.
Waiya ya jaddada cewa gwamnati na shirin tattaunawa da dukkan masu ruwa da tsaki, tare da bin doka, mutunta cibiyoyin gargajiya da kuma kare muradun al’ummar Kano baki ɗaya.
Ya buƙaci al’ummar Kano su kwantar da hankalinsu tare da tabbatar da cewa gwamnati na ci gaba da mayar da hankali kan haɗin kai, ci gaba da shugabanci nagari.
Kwamishinan ya ce za su tabbatar da gaskiya da zaman lafiya a jihar kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta tattaro.



