DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Kotu ta soke babban taron da PDP ta yi a Ibadan tare da hana Turaki da wasu bayyana kansu a matsayin shugabannin jam’iyyar

-

Kotun Tarayya da ke Ibadan ta soke taron ƙasa na jam’iyyar PDP da aka gudanar a ranar 15 ga Nuwamba 2025 a Ibadan, Jihar Oyo, tare da hana Kabiru Turaki da wasu gabatar da kansu a matsayin shugabannin ƙasa na jam’iyyar.

Kotun ta yanke hukuncin ne a ranar Juma’a, bayan shari’o’in rikicin shugabanci da ke addabar PDP, duk da cewa jam’iyyar ta gudanar da taron zaɓe na kwanaki biyu a filin wasa na Lekan Salami da aka yi wa lakabi da Ibadan2025, inda dubban wakilai da magoya baya suka halarta.

Google search engine

Da yake mayar da martani, Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa na PDP, Ini Ememobong, ya ce jam’iyyar na jiran hukuncin kotunan ɗaukaka ƙara, inda ta bayyana cewa bangaren Kabiru Turaki na nan daram bisa doka. Ya bukaci mambobi su kwantar da hankalinsu, yana mai cewa babu dalilin fargaba.

Jam’iyyar ta ce za ta ci gaba da fafutukarta yayin da shari’ar ke gaba a kotunan ɗaukaka ƙara, lamarin da ake sa ran zai yi tasiri kan makomar PDP gabanin manyan harkokin siyasa masu zuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Hatsari ya yi ajalin mutum 5,289 a Nijeriya cikin 2025 – Hukumar FRSC

Hukumar kiyaye hadurra ta Nijeriya, FRSC, ta bayyana cewa an samu hatsarin mota 10,446 a fadin kasar a shekarar 2025, inda mutane 5,289 suka rasa...

Majalisa Dattawa ta nemi Tinubu ya kafa sansanin soji a Katsina bisa dawowar hare haren ‘yan bindiga a jihar

Majalisar Dattawan Nijeriya ta nuna matuƙar damuwa kan tabarbarewar tsaro a jihar Katsina, musamman a yankin Funtua, bayan hare-haren ’yan bindiga da suka yi sanadin...

Mafi Shahara