Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida ta Amurka ta bayyana cewa za ta kori ’yan Nijeriya ba ƙasa da 79 da aka yanke wa hukunci bisa aikata laifuka a ƙasar.
Binciken jaridar PUNCH a shafin yanar gizon DHS a ranar Litinin ya nuna cewa ’yan Nijeriyan 79 din sun samu hukunci ne kan laifuka da suka haɗa da zamba, fataucin miyagun ƙwayoyi, duka da raunatawa, kisan kai da fashi, da sauransu.
Wata sanarwa ta nuna cewa an kama mutanen ne a cikin yakin da Amurka ke yi na kama ’yan ƙasashen waje masu aikata laifuka, kafin a shirya korarsu daga ƙasar.


