Duk da samun kimanin Naira tiriliyan 9 daga rabon hukumar rarraba kudaden shiga na tarayya (FAAC) a shekarar 2025, gwamnonin jihohi na fuskantar suka daga ƙungiyoyin ƙwadago, ƙungiyoyin fararen hula da jam’iyyun adawa, bisa zargin cewa akwai tazara mai faɗi tsakanin karuwar kudaden shiga da ƙarancin ayyukan jin daɗin jama’a.
Bincike kan bayanan rarraba kudaden Asusun Tarayya da Hukumar Kididdiga ta Ƙasa (NBS) ta wallafa, wanda jaridar The PUNCH ta tattara, ya nuna cewa rabon FAAC ga jihohi ya ƙaru da sama da N2tn cikin shekara guda.
Wannan ya jawo suka daga ƙungiyoyin ƙwadago da jam’iyyun adawa.
Kungiyar Kwadago ta Nijeriya (NLC) ta yi gargaɗin cewa, duk da ƙarin kudaden da jihohi ke samu, ba a ga canji mai ma’ana a rayuwar jama’a ba, tana danganta hakan da raunin shugabanci, fifiko marar dacewa, da cin hanci da rashawa a matakin jihohi.



