Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, Gianni Infantino, ya kare matakin da ya dauka na bai wa Shugaban Amurka, Donald Trump, lambar yabo ta FIFA Peace Prize da yayi a kwanakin baya, duk da sukar da ya sha wajen mutane a sassa daban-daban na duniya.
Infantino ya yi wannan bayani ne a wata hira da jaridar Sky News a ranar Litinin, bayan ya sha suka saboda bai wa Trump lambar yabo a yayin bikin fidda jadawalin gasar kofin duniya ta 2026 da aka gudanar a Washington DC a watan Disamba.
Shugaban FIFA ya ce a ganinsa, Trump ya cancanci lambar yabon, yana mai cewa duk wani abu da zai taimaka wajen samar da zaman lafiya a duniya ya dace a ƙarfafa shi.
Ya bayyana cewa FIFA ta dade tana tunanin samar da wata lambar yabo domin karrama mutanen da ke bayar da gudunmawa ga zaman lafiya a duniya.



