DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Ba gudu ba ja da baya kan gyare gyaren tattalin arziki a Nijeriya – Shugaba Tinubu

-

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa ba gudu babu ja da baya kan gyare-gyaren tattalin arziƙi, duk da radadin da aka fuskanta a farkon aiwatar da su, yana mai jaddada aniyar ci gaba da aiwatar da wadannan manufofi.

Jaridar Punch ta raiwato Tinubu na bayyana hakan ne a ranar Talata, 4 ga Fabrairu, 2026, lokacin da ya karɓi tawagar Bankin Duniya karkashin jagorancin Anna Bjerde.

Google search engine

A cewarsa, gyare gyaren ciki har da cire tallafin man fetur da gyara farashin canjin kuɗaɗe sun kasance masu wahala da farko, amma sun zama dole domin ƙarfafa tattalin arziƙin Nijeriya, musamman don ƙirƙirar dama ga matasa masu tasowa a kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Ba sai kundin tsarin mulki ya ban dama ba, zan iya bai wa duk wani mai mulki shawara – Sarki Sunusi II

Sarkin Kano, Alhaji na 15 Muhammadu Sanusi II, ya ce ba sai kundin tsarin mulki ya ba shi dama kafin ya ba Shugaban kasa ko...

’Yan sanda sun dakile yunkurin kai hari a Zamfara, tare da kama masu bai wa ’yan bindiga bayanai

Rundunar ’yan sandan jihar Zamfara sun dakile wani yunkurin kai hari da ’yan bindiga suka yi kan titin Gusau–Talata Mafara, inda aka jikkata jami’inta guda...

Mafi Shahara