DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Ba sai kundin tsarin mulki ya ban dama ba, zan iya bai wa duk wani mai mulki shawara – Sarki Sunusi II

-

Sarkin Kano, Alhaji na 15 Muhammadu Sanusi II, ya ce ba sai kundin tsarin mulki ya ba shi dama kafin ya ba Shugaban kasa ko Gwamna shawara kan muhimman al’amuran da suka shafi ƙasa ba, yana mai jaddada muhimmancin sarakuna wajen gina ƙasa da kyakkyawan shugabanci.

Sarkin ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels Television a ranar Laraba, 4 ga Fabrairu, 2026.

Google search engine

Ya ce ikon ba da shawara yana fitowa ne daga matsayin da yake da shi a matsayin jagoran al’umma, ba wai dole sai doka ta bashi damar ba.

Sarkin ya nanata buƙatar shigar mata a siyasa da harkokin mulki, yana cewa hakan zai ƙara inganta shugabanci da haɗin kai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Jinkirin gyaran Dokar Zabe na iya shafar jadawalin zaben 2027 — INEC

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Nijeriya (INEC) ta ce jinkirin yin gyara ga Dokar Zabe na iya shafar jadawalin gudanar da zaben 2027. Shugaban INEC,...

’Yan sanda sun dakile yunkurin kai hari a Zamfara, tare da kama masu bai wa ’yan bindiga bayanai

Rundunar ’yan sandan jihar Zamfara sun dakile wani yunkurin kai hari da ’yan bindiga suka yi kan titin Gusau–Talata Mafara, inda aka jikkata jami’inta guda...

Mafi Shahara