Rundunar ’yan sandan jihar Zamfara sun dakile wani yunkurin kai hari da ’yan bindiga suka yi kan titin Gusau–Talata Mafara, inda aka jikkata jami’inta guda ɗaya yayin musayar wuta.
Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa tawagar ’yan sanda karkashin jagorancin DSP Ma’aji Ndagunu na dawowa ne daga Gusau, a lokacin da ‘yan bindigar suka yi musu kwanton bauna a kauyen Kwanar Kirya.
’Yan sandan sun mayar da martani, lamarin da ya tilasta wa maharan tserewa zuwa dazuka, ana zargin wasu sun jikkata da harsasai.
A yayin artabun, Insp. Jamilu Abdullahi ya samu rauni a cinyarsa ta dama, inda aka garzaya da shi Asibitin Talata Mafara domin jinya.



