DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Majalisar dattawa ta amince da tura sakamakon zabe kai tsaye da tsarin tuka-tuka

-

Majalisar Dattawan Nijeriya ta janye matsayinta na baya tare da amincewa da tura sakamakon zabe ta kai tsaye daga rumfunan zabe zuwa dandalin IReV na INEC, inda ta tanadi cewa idan tsarin yanargizo ya gaza, takardar EC8A za ta zama babbar hanyar tattara sakamako.

Majalisar ta dauki wannan matsaya ne a zaman gaggawa da ta yi a Abuja, bayan amincewa da kudurin da mai tsawatarwa na Majalisar, Sanata Mohammed Monguno, ya gabatar, wanda Shugaban ‘Yan Adawa, Sanata Abba Moro, ya mara wa baya.

Google search engine

Shugaban Majalisar, Sanata Godswill Akpabio, ya karanta sabon tanadin Sashe na 60(3) kafin a kada kuri’a, inda mafi yawan sanatoci suka amince da gyaran.

Sanata Monguno ya ce an dauki matakin ne domin dokar zabe ta dace da muradin ‘yan Nijeriya da kuma tabbatar da sahihin zabe mai gaskiya da adalci.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa da farko zaman ya kaure da hayaniya, bayan wasu sanatoci sun nuna rashin jin dadi da wasu kalmomi da ke cikin sabon tanadin, sai dai daga bisani Majalisar ta amince da shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

‘Yan bindiga sun hallaka manoma 32 a jihar Niger

Akalla manoma 32 ne aka hallaka a hare-haren da ’yan bindiga suka kai kan al’ummomin Tugan-Makeri, Konsoko da Pissa a karamar hukumar Borgu ta Jihar...

Peter Obi ya bukaci matasa da su nuna kauna da kishin Nijeriya albarkacin ranar masoya

Tsohon ɗan takarar shugaban Nijeriya, Peter Obi, ya bukaci ’yan Nijeriya musamman matasa su yi bikin ranar masoya ta Valentine cikin nuna kishin ƙasa da...

Mafi Shahara