Sanata mai wakiltar Babban Birnin Tarayya (FCT), Ireti Kingibe, ta zargi Ministan FCT, Nyesom Wike, da tafiyar da mulki irin na kama-karya tare da kin hada kai da masu ruwa da tsaki a yankin.
Da take magana a shirin Politics Today na Channels Television, Kingibe ta ce ministan ba ya son yin aiki tare da zababbun wakilai da jami’an gwamnati domin kai ribar dimokuradiyya ga mazauna FCT.
Ta bayyana cewa duk da wasikun da ta aike masa tana nuna shirinta na ba da hadin kai, har yanzu ba ta samu amsa mai gamsarwa ba.
Har ila yau, Kingibe ta soki matakin da ministan ya dauka na kakaba dokar hana fita ta awanni 22 gabanin zaben kananan hukumomin da ake gudanar wa a ranar 21 ga Fabrairu a Abuja.
Ministan ya ayyana ranar Juma’a a matsayin ranar hutu tare da hana zirga-zirga daga karfe 8 na dare zuwa 6 na safe washegari Asabar.



