Sufeto Janar na ’Yan sandan Nijeriya Tunji Disu, ya kaddamar da kwamitin mutum takwas domin aiwatar da tsarin kafa ’yan sandan jihohi, bayan amincewa da nadinsa a matsayin IGP na 23 a kasar.
Disu ya ce matakin na daga cikin manufofinsa na gyaran aikin ’yan sanda da karfafa tsaro a fadin kasa. An nada Farfesa Olu Ogunsakin a matsayin shugaban kwamitin.
Disu ya jaddada cewa shugabanci nauyi ne, ba mukami ba, yana mai kiran a sanya kwarewa da rikon amana tare da girmama hakkokin bil’adama a dukkanin ayyukan rundunar.
Nadin Disu ya biyo bayan amincewar Hukumar ‘Yan sanda da kuma nadin da Shugaba Tinubu ya yi masa bayan murabus din tsohon IGP, kuma ana sa ran rantsar da shi a hukumance yayin taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya.



