Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa yanzu tana da cikakken tsarin gano tare da cafke baƙin ƙasashen waje da suka wuce wa’adin zaman da aka ba su a ƙasar.
Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Abuja yayin taron nazarin ayyukan ma’aikatar cikin gida na shekarar 2026.
Ministan ya ce gwamnati yanzu tana da cikakkun bayanan dukkan mutanen da suka shiga Nijeriya cikin shekaru goma da suka gabata, wanda hakan ke ba jami’an gwamnati damar gano waɗanda suka karya dokar zaman ƙasar.
Ya ce an samu wannan cigaba ne bayan kafa cibiyoyin kula da ayyuka na zamani a hukumar kula da shige da fice ta Nijeriya.



