Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana cikakken goyon bayan kasarsa ga Najeriya wajen yaki da matsalar tsaro, musamman barazanar ta’addanci da ake fuskanta a Arewa.
A wani saƙo da ya wallafa a X a ranar Lahadi, Macron ya ce ya yi magana da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, inda ya tabbatar masa cewa Faransa za ta ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa da gwamnatin Najeriya.
Sanarwar ta Macron na zuwa ne bayan ƙarin hare-hare da garkuwa da mutane a yankin Arewa, lamarin da ya ja hankalin ƙasashen duniya.
Najeriya na ci gaba da neman goyon bayan ƙasashen duniya, ciki har da tattaunawar da Mai bai wa Shugaban kasa shawara kan tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, ya yi da Sakataren harkokin Yaƙin Amurka, Pete Hegseth, a Pentagon domin inganta dabarun yaki da ta’addanci a Nijeriya.



