Kungiyar ECOWAS ta ayyana dokar ta-baci a yankin Yammacin Afirka, sakamakon ƙarin tabarbarewar tsaro da kuma yawaitar juyin mulki a wasu ƙasashen mamba.
Shugaban Hukumar ECOWAS, Omar Touray, ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin zaman kwamitin sulhu na majalisar karo na 55 na matakin ministoci da aka gudanar a Abuja.
Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa Touray ya ce halin da ake ciki ya nuna buƙatar yin nazari mai zurfi kan makomar dimokuraɗiyya a yankin, tare da ƙara zuba jari a fannin tsaro don kare al’ummomin ƙasashe mambobin kungiyar.
Majiyar DCL Hausa ta ruwaito cewa taron ya gudana ne a daidai lokacin da ake fama da juyin mulki a Guinea-Bissau, Mali, Burkina Faso da Nijar, tare da ƙoƙarin kifar da gwamnati a Jamhuriyar Benin da wasu sassan yankin, lamarin da ya ƙara tayar da hankalin shugabanni.



