Akalla sabbin kananan sojojin Nijeriya 3,439 ne suka kammala horo a cibiyar horas da sojoji ta Nijeriya da ke Zariya.
Sabbin sojojin, wadanda ke cikin rukuni na 89 na daukar sojoji na yau da kullum, sun shafe watanni shida suna horo kafin a gabatar da su a bikin fitar da su wato Passing Out Parade da aka gudanar ranar Juma’a. Bayan kammala horon, za a tura su sassa daban-daban na kasar domin gudanar da ayyukansu.
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar sojojin kasa, Kanal Appolonia Anele, ta fitar, ta ce Babban Hafsan Sojin Kasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya bukaci sabbin sojojin da su rungumi biyayya, ladabi da kwarewa yayin da suke shiga aikin kasa, yana mai cewa karin adadinsu zai kara karfin rundunar wajen tinkarar barazanar tsaro a cikin gida da ma ketare.



