Shugaba Tinubu ya bukaci majalisa ta sahale masa nada sabbin shugabannin hukumomin kula da man fetur bayan da Injiniya Farouk Ahmed, ya yi murabus a matsayin shugaban Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Nijeriya, tare da takwaransa Gbenga Komolafe, shugaban Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Sama (NUPRC).
Dukkaninsu tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya nada su a shekarar 2021, bayan kafa hukumomin karkashin Dokar Man Fetur ta PIA.
Wannan na zuwa ne bayan zargin da attajirin dan kasuwa Aliko Dangote ya yi wa Farouk Ahmed, na rayuwa fiye da karfin albashin ma’aikacin gwamnati, musamman dangane da kudaden da ake zargin ya kashe wajen karatun ’ya’yansa a kasar Switzerland.
Zargin ya haifar da muhawara Dangote ya hakikance cewa akwai bukatar bincike inda ya gabatar da korafi a gaban Hukumar ICPC.
Sai dai a cikin sanarwar ta fito ne daga Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Kan Yada Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya ce Shugaba Tinubu ya nada Injiniya Saidu Aliyu Mohammed a matsayin shugaban NMDPRA, tare da Oritsemeyiwa Amanorisewo Eyesan a matsayin shugabar NUPRC.
Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bukaci Majalisar Dattawa ta gaggauta tantance tare da amincewa da nadin sababbin shugabannin manyan hukumomin kula da harkokin man fetur da iskar gas na kasa.


