DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Ma’aunin tattalin arziki GDP na Nijeriya ya karu da kashi 3.46 – hukumar kididdiga NBS

-

Hukumar kididdiga ta kasa NBS ta ce ma’aunin tattalin arzikin Nijeriya ya karu zuwa kashi 3.46 a rubu’i na uku na shekarar 2024, inda ya kai naira tiriliyan 71.1.
Wani bayani da Shugaban hukumar kididdiga ta kasa Prince Adeyemi Adeniran Adedeji, ya ce an samu ci gaba da kashi 0.92 idan aka kwatanta da rubu’i na uku na shekara ta 2023 da ma’aunin GDP ya kai kashi 2.54.
Bayanin ya kara da cewa ma’aunin a rubu’i na uku ya yi sama da kashi 0.27 idan aka kwatanta da rubu’i na biyu na wannan shekara ta 2024.
Wannan ci gaban da aka samu, hukumar kididdiga NBS ta alakanta shi da ci gaban da aka samu fannin noma da kasuwanci da sadarwa da kuma harkar gidaje.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Wasu lauyoyi biyu daga Tanzania sun yi kara a gaban kotu suna kalubalantar zaɓen 2025 da aka gudanar a kasar

Wasu lauyoyi biyu a Tanzania, Tito Magoti da Bob Wangwe, sun kai ƙasar Tanzania gaban Kotun Gabashin Afirka kan zaɓen da aka gudanar a ranar...

Za mu karbi Peter Obi hannu biyu a jam’iyyar LP idan bai samu takara a ADC ba – Datti Baba Ahmed

Tsohon ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party LP,Yusuf Datti Baba-Ahmed, ya bayyana cewa Peter Obi zai samu tarba a LP idan har...

Mafi Shahara