Ƙungiyar Ƙananan Hukumomi ta Nijeriya (ALGON) da Ƙungiyar Ma’aikatan Ƙananan Hukumomi (NULGE) sun mara wa Shugaban Nijeriya Bola Tinubu baya kan shirin tilasta biyan kuɗaɗen ƙananan hukumomi kai tsaye daga asusun gwamnatin tarayya.
Tinubu ya yi gargaɗin cewa zai fitar da umarni na shugaban ƙasa idan gwamnonin jihohi suka ƙi bin hukuncin Kotun Ƙoli.
Kotun Ƙoli a ranar 11 ga Yuli, 2024 ta haramta wa jihohi riƙe ko sarrafa kuɗaɗen ƙananan hukumomi, tare da bayyana tsarin kwamitin rikon ƙwarya a matsayin saɓa wa Kundin Tsarin Mulki. Duk da haka, har yanzu ba a aiwatar da hukuncin gaba ɗaya ba.
Binciken The PUNCH ya nuna cewa jihohi sun cigaba da sarrafa Naira tiriliyan 7.43 na kuɗaɗen ƙananan hukumomi daga Yuli 2024 zuwa Disamba 2025, duk da umarnin biyan kuɗaɗen kai tsaye.



