Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya ce saɓanin da ke tsakaninsa da Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya samo asali ne daga furucin Wike na cewa zai “riƙe PDP” domin taimaka wa Shugaba Bola Tinubu sake cin zaɓe a 2027.
Makinde ya bayyana hakan ne a wata hira da manema labarai a Ibadan, inda ya ce ya yi mamaki lokacin da Wike ya faɗi hakan a gaban Shugaba Tinubu, alhali shugaban Nijeriyar bai nema ba kuma bai amince da hakan ba. Ya ce Wike na da ’yancin goyon bayan Tinubu, amma bai kamata ya hana sauran ’yan PDP kare jam’iyyar da dimokuraɗiyya ba.
Sai dai mai taimaka wa Wike kan harkokin yaɗa labarai, Lere Olayinka, ya caccaki Makinde, yana cewa gwamnan Oyo mutum ne mai bin son zuciyarsa kawai ba tare da biyayya ga jam’iyya ko mutum ba kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Olayinka ya zargi Makinde da sauya jam’iyya sau da dama saboda muradin kansa, yana mai cewa bayan zaɓen 2027 ma, Makinde zai sake ficewa daga PDP.



