Fadar Shugaban Nijeriya ta karyata jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya maye gurbin Shugaban Ma’aikatansa, Hon. Femi Gbajabiamila, da Sakatarensa, Hakeem Muri-Okunola.
A wata sanarwa da Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai da Tsare-tsare, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar 25 ga Disamba, ya ce labarin ƙarya ne tsagwaronsa, inda ya jaddada cewa Gbajabiamila na nan daram a kan muƙaminsa.
Sanarwar ta ƙara da cewa Hakeem Muri-Okunola ma yana nan a matsayinsa na “Principal Private Secretary”, tana mai kira ga ’yan Nijeriya da su yi watsi da labaran bogi, tare da gargaɗin kafafen yaɗa labarai su rika tantance sahihancin bayanai kafin wallafawa.



