Kotun Tarayya da ke Abuja ta umurci Hukumar EFCC da ta gabatar da Kwamishinan Kuɗin Jihar Bauchi, Yakubu Adamu, a ranar 30 ga Disamba domin gurfanar da shi kan zargin safarar kuɗi har Naira biliyan 4.6.
Mai shari’a Emeka Nwite ya bayar da umarnin ne a ranar Laraba, bayan EFCC ta kasa gabatar da Adamu domin karɓar tuhuma karo na biyu a gaban kotu.
EFCC ta zargi Adamu da kamfanin Ayab Agro Products and Freight Company Ltd da haɗa baki wajen safarar N4.65bn tsakanin Yuni da Disamba 2023, lokacin da yake reshen Manajan Polaris Bank a Bauchi, tare da wasu mutane biyu da ake nema ruwa a jallo.
Lauyoyin wanda ake tuhuma sun koka kan ci-gaba da tsare Adamu ba tare da gurfanar da shi ba, suna cewa hakan na shafar ayyukan gwamnati, musamman biyan albashin ma’aikata a jihar, yayin da kotu ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar 30 ga Disamba.



