Thursday, April 9, 2026
HomeUncategorized'Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 6,tare da halaka wani manomi...

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 6,tare da halaka wani manomi a Taraba

Gwamnan jihar Taraba Agbu Kefas

‘Yan bindigar dai sun halaka manomin mai suna Alhaji Mai Wanda Maibultu a gonar sa a karshen makon da ya gabata,wanda yana daya daga cikin manyan manoma a kauyen.

Daily Trust ta rawaito cewa sauran manoma shidan da aka yi garkuwa da su,suna kauyen Garbatau, da ke tsakanin tsaunuka biyu a yanki.

Wani mazaunin garin Maihula, Adamu Dauda, ​​ya shaida wa Daily Trust cewa masu garkuwa da mutanen sun nemi iyalan manoman da suka sace, inda suka nemi Naira miliyan 100 a matsayin kudin fansa.

Ya ce, ko a shekarar da ta gabata daruruwan masu garkuwa da mutane sun addabi yankin tare da yin garkuwa da manoma da dama, inda suka hana su girbin amfanin gonakinsu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata