DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Gwamnatin Nijeriya za ta gina kananan tashoshin samar da lantarki a jami’o’i

-

 Gwamnatin Nijeriya ta sanar da shirin samar da sabbin kananan tashoshin samar da hasken wutar lantarki masu amfani da hasken rana a harabar manyan makarantu da asibitocin koyarwa a fadin kasar don rage tsadar wutar lantarki

Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, ya bayyana haka a lokacin da yake duba aikin Advanced Solar Microgrid a Jami’ar Abuja, wanda ya ce an kammala kashi 95 cikin 100.

Ya ce kirkirar wadannan kananan tashoshi zai taimaka sosai wajen ganin an kawo karshen tsaiko da matsalar lantarki da ake fama a wuraren 

Nijeriya dai fama da matsalar lalacewar lantarki a sakamakon yawan samun matsala da babbar tashar samar da lantarki take yi lokaci zuwa lokaci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Kai ne babban ‘butulu’, sakon NNPP ga Kwankwaso in ji jaridar Punch

Jam’iyyar NNPP ta soki Engr Rabiu Kwankwaso bisa kiran wasu ‘yan Kwankwassiyya da suka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC da sun yi butulci, jam'iyyar tana...

Tattalin arzikin Nijeriya na kara bunkasa duk kuwa da hauhawar farashin kaya – Bankin Duniya

Bankin Duniya ya bayyana cewa tattalin arzikin Nijeriya na bunkasa a cikin kusan shekaru goma a shekarar 2024. Hakan na zuwa ne sakamakon kyakkyawan ci gaba...

Mafi Shahara