Wasu lauyoyi biyu a Tanzania, Tito Magoti da Bob Wangwe, sun kai ƙasar Tanzania gaban Kotun Gabashin Afirka kan zaɓen da aka gudanar a ranar 29 ga Oktoba, 2025, suna zargin cewa zaɓen bai cika ka’idojin dimokuraɗiyya da dokoki ba.
A ƙarar da suka shigar, lauyoyin sun gurfanar yi karar Antoni Janar na Tanzania da kuma Sakataren Janar na kungiyar kasashen Gabashin Afirka (EAC), inda suka ce zaɓen ya saɓa wa tanade-tanaden yarjejeniyar kungiyar, musamman waɗanda suka shafi dimokuraɗiyya.
Lauyoyin sun jaddada cewa yadda aka gudanar da zaɓen ya tauye waɗannan ka’idoji, lamarin da a cewarsu ya sanya sakamakon ya zama abin tambaya a idon doka da ƙa’idar dimokuraɗiyya a yankin Gabashin Afirka.



