Jam’iyyar APC a jihar Kano ta bayyana cewa tana maraba da Gwamna Abba Kabir Yusuf bayan ficewarsa daga NNPP, tana mai nuna fatan zai sanar da shigarsa jam’iyyar nan ba da jimawa ba. Sakataren APC na jihar, Ibrahim Zakari Sarina, ne ya bayyana hakan yayin da yake amsa tambayoyi kan matakin da gwamnan zai ɗauka na gaba.
Sarina ya ce kodayake gwamnan bai sanar da shigarsa APC a hukumance ba, jam’iyyar na sa ran hakan zai faru, inda ya jaddada cewa ƙofofin APC a buɗe suke gare shi da magoya bayansa. Ya ƙara da cewa wannan ci gaban na ƙara ƙarfi ga jam’iyyar, ganin yadda ake tsammanin gwamnan zai zo tare da zaɓaɓɓun jami’ai da masu riƙe da muƙamai.
Ya kuma bayyana cewa APC ta riga ta ɗauki matakai na musamman domin karɓar gwamnan, inda ta tanadi lambar rajistar e-registration ta musamman mai lamba 001 a mazabarsa ta Chiranci-Diso. A cewarsa, shirin karɓar ba gwamnan kaɗai ya shafa ba, har da mambobin majalisarsa, masu goyon bayansa da dukkan abokan tafiyarsa na siyasa.



