Hukumar shari’a a Australia ta soke lasisin aikin jinya na wata ‘yar asalin Nijeriya, Chimzuruoke Okembunachi, bayan an same ta da laifin yin barci sau da dama a bakin aiki yayin aikin dare a wata cibiyar kula da tsofaffi, lamarin da ya jefa lafiyar marasa lafiya cikin hatsari.
Rahoton Daily Mail ya ce kotun NSW Civil and Administrative Tribunal ta yanke hukunci a ranar 20 ga Janairu, 2026, cewa abin da Okembunachi ta aikata a watan Maris 2024 ya kai matsayin laifin saba dokar kwarewar aiki, wanda ya sa aka cire sunanta daga rajistar ma’aikatan jinya.
Okembunachi, mai shekaru 25, ta fara aiki a Hardi Aged Care da ke Guildford a Yammacin Sydney a watan Fabrairu 2024. Kasa da wata guda bayan haka aka dakatar da ita, daga bisani kuma ta yi murabus. A zaman kotu, an bayyana cewa tsakanin 13 zuwa 27 ga Maris, ita ce kaɗai babbar ma’aikaciyar jinya a aikin dare, tana kula da mataimakan jinya uku ko hudu da kuma kusan tsofaffi 100.
An tabbatar da cewa a akalla darare shida ta kasa gudanar da aikinta saboda barci, yayin da marasa lafiya uku suka rasa shan magungunan morphine a kan lokaci. A wani lokaci, an ce ta umarci wata mataimakiyar jinya da ba ta da izini ta ba mara lafiya Panadol.
Kotun ta ce duk da ta nuna nadama, abin da ta aikata na da barazanar jefa rayukan marasa lafiya cikin hatsari, don haka dole ne a soke lasisinta. An hana ta neman sake dubawa na tsawon akalla watanni tara. Duk da haka, tana ci gaba da karatun likitanci a Jami’ar Western Sydney, tana samun tallafi daga mahaifinta da kuma taimakon dalibai na Centrelink.



