DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Da Dumi-Dumi: Shugaba Tinubu ya umurci a saki yaran da aka kama yayin zanga-zangar tsadar rayuwa a Nijeriya

-

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya bayar da umarnin sakin duk wasu kananan yara da aka kama da kuma tsare su saboda zanga-zangar tsadar rayuwa a Nijeriya.

Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Litinin

Google search engine

Muhammad Idris ya ce shugaban kasar ya umurci babban lauyan gwamnatin tarayya, Lateef Fagbemi, da ya gaggauta fara aikin ganin an sako yaran domin haduwa da iyalansu.

An kuma kafa wani kwamiti da zai duba hanyoyin da aka bi wurin kama su tare da tsare su domin yi masu adalci

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Mo Salah ya kafa tarihi a Firimiya inda ya zama dan wasa mafi ba da gudummuwar kwallaye a kulob daya

Dan wasan Liverpool, Mohamed Salah, ya karya tarihin mafi yawan gudummawar kwallaye (zura kwallo da bayarwa) da dan wasa ya taba yi wa kungiya daya...

Duk inda dan Nijeriya yake bai da wuyar ganewa saboda izza da kwarin guiwa a tafiyarsa da mu’amalarsa – Kashim Shettima

Mataimakin Shugaban Nijeriya, Kashim Shettima, ya ce ana iya gane dan Nijeriya a ko’ina cikin duniya, ciki har da London, saboda irin izza da kwarin...

Mafi Shahara