Tuesday, April 7, 2026
HomeUncategorized'Yan bindiga sun sace matafiya da dama a hanyar Mariga-Kontagora jihar Niger

‘Yan bindiga sun sace matafiya da dama a hanyar Mariga-Kontagora jihar Niger

 

Rahotanni daga jihar Niger na cewa masu garkuwa da mutane sun sace akalla fasinjoji 20 da suke a cikin motoci biyar yayin da suke kan hanyar Mariga zuwa Kontagora.

Kakakin majalisar dokokin jihar Neja mai wakiltar mazabar Mariga, Abdulmalik Sarkin-Daji, ya tabbatar da hakan a wata hira da ya yi da manema a ranar Juma’a a garin Minna babban birnin jihar.

Ya ce lamarin ya faru ne a ranar Alhamis yayin da ‘yan bindiga suka tare hanyar Mariga zuwa Kontagora tsakanin Baban-Lamba da Beri.

Jihar Niger da daya daga cikin jihohin da ke fama da matsalar tsaro a Arewacin Nijeriya 

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata