Rahotanni na nuni da cewa an tilasta wa Sufeto Janar na ‘yan Sandan Nijeriya, Kayode Egbetokun, yin murabus daga muƙaminsa bisa umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, kamar yadda majiyoyi daga fadar shugaban ƙasar suka tabbatar.
Jaridar Premium times ta rawaito cewa majiyar ta ce an bukaci Egbetokun ya ajiye muƙaminsa ne a wani taro da aka yi da shugaban ƙasa a fadarsa a ranar Litinin.
An kuma bayyana cewa ana shirin nada mataimakin Sufeto Janar na ‘yan Sanda AIG, Tunji Disu, domin maye gurbinsa, amma har zuwa lokacin kammala wannan rahoto ba a fitar da sanarwar nadin nasa a hukumance ba.



