Rahotanni na nuna cewa akalla ministoci hudu a gwamnatin Bola Ahmed Tinubu na shirin ajiye mukamansu domin neman wasu mukaman siyasa a jihohinsu gabanin babban zaben 2027.
Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa daga cikin ministocin da ake zargin suna da wannan buri akwai ministan wutar lantarki Adebayo Adelabu, ministan lafiya Muhammad Ali Pate, ministan harkokin waje Yusuf Maitama Tuggar, da kuma karamin ministan kwadago Nkeiruka Onyejeocha.
Bincike ya nuna cewa wadannan ministoci na duba yiwuwar tsayawa takarar gwamna ko kuma wasu mukaman siyasa a jihohinsu, musamman a jihohin da gwamnoni za su kammala wa’adin mulkinsu na biyu a shekarar 2027.
Dokar zabe ta tanadi cewa duk wani mai rike da mukamin gwamnati da aka nada dole ne ya ajiye mukaminsa kafin ya shiga zaben fidda gwani a kowace jam’iyya.



