Shugaban kamfanin mai na NNPCL, Bayo Ojulari, ya ce warware rikicin OPL 245 zai ba Najeriya damar kara ganga 150,000 na mai a rana.
Ya bayyana cewa hakan zai bai wa aikin Zabazaba–Etan deepwater project damar fara aiki.
Gwamnatin Nijeriya ta kulla yarjejeniya da Eni da kuma Nigerian Agip Exploration Limited domin kawo karshen rikicin mai na sama da shekaru 15.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ce warware matsalar na nuna wa masu zuba jari na duniya cewa Najeriya na shirye ta magance tsoffin matsaloli tare da bude damar sabbin kafofin zuba jari a bangaren makamashi.



