Monday, April 6, 2026
HomeUncategorizedSojoji sun hallaka 'yan bindiga masu tarin yawa a Giwa jihar Kaduna

Sojoji sun hallaka ‘yan bindiga masu tarin yawa a Giwa jihar Kaduna

Rahotanni daga karamar hukumar Giwa jihar Kaduna na cewa sojoji sun yi nasarar hallaka ‘yan bindiga masu tarin yawa a wani harin da suka kai a yankin.
Wannan harin da sojoji suka kai ta sama da kasa ya yi sanadiyyar mutuwar ‘yan bindigar, ciki kuwa hada wasu daga cikin jagororinsu a yankin Bula a cikin Dajin Yadi na karamar hukumar ta Giwa a jihar Kaduna.
Kamar yadda sako ya isa ga gwamnatin jihar Kaduna, an kai wannan harin ne biyo bayan wasu bayanan sirri da aka samu bayan kashe wasu jiga-jigan ‘yan bindiga a kan iyakar Kaduna-Katsina.
Bayanan sirrin dai sun ce ‘yan bindigar sun hadu a Dajin Yadi ne domin su kitsa yadda za su farmaki al’ummomi daban-daban na jihar. Bayan samun wannan bayani, jami’an tsaro suka kimtsa suka tunkare su yadda ya kamata, kuma suka yi nasarar yin fata-fata da su.
Bayanin hakan dai na cikin wata sanarwa daga kwamishinan tsaro da lamurran cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan da DCL Hausa ta samu kwafi.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata