DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Gwamnatin jihar Kano ta rufe wuraren kasuwanci 9 saboda ƙin biyan haraji

-

Jami’an hukumar tattara haraji ta jihar Kano sun rufe wuraren kasuwanci na wasu kamfanoni tara bisa zargin kin biyan kudaden haraji.
Daga cikin wuraren da aka rufe har da makarantu da wasu wuraren kasuwanci yayin zagayen rufe wuraren da tawagar KIRS ta gudanar.
A cewar jagoran tawagar jami’an hukumar Abbas Sa’idu, matakin da hukumar ta dauka ya zama dole domin kamfanonin sun kasa amsa wasikun da hukumar ta aika musu, tare da sanar da su kan bukatar biyan kudaden harajin da ake bin su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

‘Bai kamata NAHCON ta fara shirin hajjin 2026 ba tare da ta bayar da bayanin kudaden da aka kashe a hajjin 2025 ba‘

Ƙungiyar Shugabannin Hukumomin Jin Dadin Alhazai ta Jihohin Nijeriya ta bukaci hukumar kula da aikin hajji ta Nijeriya (NAHCON) da ta gaggauta kammala daidaita bayanan...

Farfesoshin Nijeriya na cikin jerin na nahiyar Afrika da ba su da albashi mai kyau

Bayanan da jaridar Punch ta tattaro sun ce malamin jami'a a Nijeriya da ya kai matakin farfesa na samun matsakaicin albashi na dala 366 (kimanin...

Mafi Shahara