DCL Hausa Radio
Kaitsaye

NAHCON ta aike da ma‘aikatan farko da za su tarbi maniyyata zuwa Saudiyya

-

Tawagar ma’aikata 43 daga hukumar kula da aikin hajji ta Nijeriya NAHCON za su tashi daga Abuja a gobe Lahadi, zuwa kasar Saudiyya, domin murnar tarbar jirgin farko na mahajjatan Nijeriya a kasar Saudiyya.
Tawagar da ta kunshi jami’an hukumar NAHCON 35 da ma’aikatan lafiya 8 za su je kasar Saudiyya domin shirin karshe na karbar mahajjatan Nijeriya daga jihar Kebbi da za su isa Saudiyya a ranar Laraba 15 ga watan Mayu domin gudanar da aikin Hajjin bana na shekarar 2024.
Da yake jawabi ga tawagar a wani dan takaitaccen biki na ban kwana da aka gudanar a dakin taro na hukumar, Abuja, shugaban hukumar Malam Jalal Ahmad Arabi ya gargadin cewa hukumar za ta dauki tsattsauran mataki a kan duk wanda aka samu rahoton ya kauce wa ka’idar aiki ga amanar da aka dora musu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Kamfanin NNPCL ya musanta labarin cefanar da matatar man birnin Port Harcourt

Kamfanin man fetur na Nijeriya NNPCL ya musanta labarin cefanar da matatar mai ta Fatakwal ga yan kasuwa A Yayin wani taro da kamfanin ya gabatar...

Tattalin arzikin Najeriya zai bunkasa daga 2025 zuwa 2026 – IMF

Asusun Lamuni na Duniya (IMF) ya sabunta hasashensa kan ci gaban tattalin arzikin Najeriya, inda ya ce zai kai kashi 3.4 cikin 100 a shekarar...

Mafi Shahara