Donald Trump, ya ce wayoyin hannu na kasar China da sauran na’urorin lantarki ba za a cire su daga biyan haraji ba.
Kasuwannin hannayen jari na Turai sun yi tashin gwauron zabi a safiyar Litinin din nan bayan sanarwar da Trump ya fitar a ranar Juma’a a hukumance cewa wasu daga cikin wadannan kayayyaki za su kauce wa harajin da ya kai kashi 145%.