DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Farashin abinci na kara ruda ‘yan Nijeriya

-

Farashin wasu kayan abinci na sauka na wasu na hawa a wasu kasuwannin sassan Nijeriya a daidai lokacin da al’umma da dama da ke faɗin ƙasar ke fama da karancin man fetur da rashin wutar lantarki da ma batun Dala da ya dabaibaye sassan rayuwa daban-daban.

A wannan makon masara ta fi tsada a Kasuwar Mile 12 International Market da ke Legos da aka saida ₦65,000, yayin da a makon da ya gabata aka sayar ₦60,000 daidai, an samu karin ₦5000 a makon nan.
Sai kuma kasuwar Gombi da ke jihar Adamawa, inda a wannan makon aka sayi buhun Masarar ₦57-60,000, bayan da a makon jiya aka sayar ₦45-47,000.
A nan ma an samu karin kusan 13,000,a mako ɗaya kacal.
Ita ma dai Kasuwar Giwa da ke jihar Kaduna, ana sayar da Masara ₦57,000 a wannan makon da ke shirin karewa, amma a makon jiya ₦53,000 aka sai da buhun masarar.
To a kasuwar Mai’adua jihar Katsina kuma ₦58,000 kuɗin buhun yake a makon da ya wuce, sai dai a makon nan kuɗin buhun ₦62,000 ne, an samu karin 4000, kenan a kasuwar Mai’adua jihar Katsina a wannan mako.
Masara ta fi sauki a kasuwar Kashere da ke jihar Gombe sama da sauran kasuwannin kasar a wannan makon, inda aka sai da buhun masara ₦55,000, sai dai makon jiya ₦50,000 kuɗin buhun yake a Kasuwar.
Haka nan a kasuwar Dawanau da ke jihar Kano ma an samu karin 4000, kan farashin makon jiya da saida ₦54,000, amma a makon nan ₦58,000 kuɗin buhun yake a kasuwar.
Ita kuwa shinkafar Hausa ta fi tsada a kasuwar Kashere da ke karamar Hukumar Akko a jihar Gombe, da aka saida buhun ₦120-130,000, bayan da aka saya ₦105-115,000, a makon da ya wuce.
Amma a kasuwar Giwa da ke jihar Kaduna kuwa shinkafar Hausar ta ɗan sauka, an dai sai da buhun shinkafar ₦125,000 a makon jiya, yayin da a makon nan kuɗin buhun ya kama ₦120,000 cif, an samu ragowar ₦5000 kenan kan farashin na baya .
Shinkafar Hausar ta faɗi a kasuwar Girie da ke jihar Adamawa da aka sai da ₦110,000, bayan da a makon jiya aka sayar ₦125,000.
Da DCL HAUSA ta leka kasuwar Mile 12 International Market da ke Legos kuwa kuɗin buhun Shinkafar ‘yar gida ₦120,000 ne a wannan makon, yayin da a makon jiya aka sai da ₦125,000.
Hakazalika a kasuwar Mai’adua jihar Katsina ma ₦120,000 aka sai da buhun shinkafar a makon nan,sai dai a makon jiya ₦105,000 aka sai da buhun, hakan na nuni cewa shinkafar ta haura a makon nan.
To a kasuwar Dawanau da ke jihar Kano an sayi shinkafar 113,000 a makon da ya gabata, amma a makon nan,₦118,000 aka sai da buhun, an samu karin ₦5000 kenan a makon nan da ke dab da ƙarewa.
Shinkafar waje kuwa ta fi sauki a wannan satin a kasuwar Zamani da ke jihar Adamawa, da ake sayarwa ₦55,000, bayan da makon da ya gabata aka sai da ₦70,000 daidai.
A jihar Gombe da ke makwabtaka da jihar Adamawa, an sayi shinkafa ‘yar waje kan kuɗi ₦62-65,000
An samu karin ₦2000 kenan kan farashin makon da ya gabata da aka sai da ₦62-63,000.
₦65,000 ake sai da buhun shinkafar Bature a kasuwar Mile 12 International Market da ke Legos a makon da ya shude, haka nan farashin bai sauya zani ba a wannan makon.
A kasuwar Giwa da ke jihar Kaduna kuwa, an sayi buhun Shinkafar waje ₦68,000 a makon da ya kare, amma makon nan ₦65,000 kuɗin buhun Shinkafar.
Sai dai fa a kasuwar Mai’adua kudin Buhun shinkafar Bature bai canza zani ba a satin nan,inda ake sai da buhun₦62,000 haka batun yake a wannan makon.
To bari mu kammala Farashin Shinkafar Baturen da Kasuwar Dawanau a jihar Kano da ke Arewacin Najeriya,an sayi buhun Shinkafar waje ₦62,000 a makon jiya, sai dai a satin nan ₦71,000 aka sai da buhun, an samu karin kudi har ₦11,000 a mako guda kawai, wanda aka danganta hakan da tashin farashin CFA a kasar.
A bangaren Taliyar Spaghetti kuwa ta fi tsada a kasuwannin jihohin Kano da Kaduna, ina aka sayi kwalin taliyar ₦14,000 a kasuwar Dawanau a jihar Kano, hakan nan a kasuwar Giwa da ke jihar Kaduna ma ₦14,000 ne kuɗin Kwalin taliyar a makon nan,an samu karin dubu guda kenan kan farashin makon jiya a kasuwar giwa da ke jihar Kaduna, amma a kasuwar Dawanau kuwa₦13,500 ne ake sai da kwalin taliyar a makon jiya.
Kwalin taliyar ya fi sauki a kasuwar Zamani da ke jihar Adamawa da aka saya kan kuɗi ₦12,700 a makon nan,yayinda aka sayi kwalin ₦13,000 a makon daya shude,an samu sassaucin 300 kenan a kasuwar.
A Mai’adua jihar Katsina ₦13,700 ake saida kwalin taliyar a makon nan, amma a makon jiya ₦13,500 aka sai da, nan ma karin ₦200 kenan aka samu a satin nan.
Ita kasuwar Mile 12 International Market da ke Legos ana sayar da kwalin taliyar ₦13,000 cif, bayan da a makon daya kare aka sayar ₦13,500.
A karshe sai kasuwar Kashere dake jihar Gombe, an sayi kwalin taliyar kan kuɗi ₦12,600 a makon nan, hakan batun yake a makon da ya kare.
DCL HAUSA A’isha Usman Gebi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Kamfanin NNPCL ya musanta labarin cefanar da matatar man birnin Port Harcourt

Kamfanin man fetur na Nijeriya NNPCL ya musanta labarin cefanar da matatar mai ta Fatakwal ga yan kasuwa A Yayin wani taro da kamfanin ya gabatar...

Tattalin arzikin Najeriya zai bunkasa daga 2025 zuwa 2026 – IMF

Asusun Lamuni na Duniya (IMF) ya sabunta hasashensa kan ci gaban tattalin arzikin Najeriya, inda ya ce zai kai kashi 3.4 cikin 100 a shekarar...

Mafi Shahara