DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Ba mu karbi takarda a hukumance daga kasashen Nijar, Mali da Burkina Faso ba – ECOWAS

-

Kungiyar kasashe masu tattalin arziki ta ECOWAS ta ce har yanzu ba ta karbi wata sanarwa ko takarda a hukumance da ke nuna sun fice daga cikin kungiyar.
A cikin wata sanarwa daga sakatariyar kungiyar ta ce kawai abin da ta sani shi ne tana aiki ba gajiyawa wajen maido da kasashen bisa turbar dimokradiyya.
Ta sanar cewa har yanzu kasashen na da matukar amfani a tafiyar da lamurran kungiyar.
A ranar Lahadin nan dai, kasashen uku na Mali, Nijar da Burkina Faso suka sanar cewa sun fice daga kungiyar ta ECOWAS inda suka ce ana musu barazana. Kasashen uku dai na karkashin jagorancin sojoji bayan da suka hambarar da gwamnatin farar hula.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Kamfanin NNPCL ya musanta labarin cefanar da matatar man birnin Port Harcourt

Kamfanin man fetur na Nijeriya NNPCL ya musanta labarin cefanar da matatar mai ta Fatakwal ga yan kasuwa A Yayin wani taro da kamfanin ya gabatar...

Tattalin arzikin Najeriya zai bunkasa daga 2025 zuwa 2026 – IMF

Asusun Lamuni na Duniya (IMF) ya sabunta hasashensa kan ci gaban tattalin arzikin Najeriya, inda ya ce zai kai kashi 3.4 cikin 100 a shekarar...

Mafi Shahara