DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Abinda na gaya wa Shugaba Tinubu kan ziyarata a Nijar – Abdulsalami Abubakar

-

Tsohon shugaban
Najeriya Abdulsalam Abubakar ya sanar da mikawa shugaban kasar Bola Ahmad
Tinubu rahoto kan batutuwan da suka tattauna yayin ziyarar tawagar da ya
jagoranta zuwa jamhuriyar Nijar.

Google search engine

Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan
kammala ganawar sa da shugaban kasa, Abdulsalam Abubakar ya ce dukkanin alamu
sun nuna cewa yaki ba zai shawo kan al’amarin ba, a maimakon haka kamata ya yi
a rungumi tattaunawar diplomasiyya.

Ganawar ta su ta sami halarcin shugaban majalisar
zartaswar kungiyar ECOWAS Dr Omar Touray da kuma babban mai baiwa shugaban
Najeriya shawara kan harkokin yada labarai Malam Nuhu Ribadu.

Bayan kammala ganawar ta su, shugaban Najeriya Tinubu
wanda kuma shine shugaban ECOWAS ya sha alwashin yiwa rahoton Nazari na tsanaki,
kafin daga bisani kuma a san matakin da za’a dauka.

Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da ECOWAS ta
sanar da cewa ta gama duk wani shiri na fadawa Nijar da yaki.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Yan kasuwar mai sun sauke farashin man fetur kasa da yadda Dagote ke sayarwa

Wasu masu shigo da man fetur daga ƙasashen waje sun fara sayar da shi a ƙasa da Naira 860 kowace lita, lamarin da ya sauka...

Saurayi ya gaggabe wa budurwarsa hakora shida a Legas

Wani saurayi a unguwar Ibadan dake Ebute Meta, jihar Legas, ya lakadawa budurwarsa Fatima, wadda ke sana’ar gyaran kai, dukan da ya janyo ta rasa...

Mafi Shahara