DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Paparoma ya yi kyakkyawan karshe – Tinubu

-

Da zuciya mai nauyi, na shiga cikin Kiristoci na Katolika da sauran mabiya addinin Kirista a duniya wajen jimamin rasuwar Paparoma Francis — bawan Allah mai tawali’u, mai himma wajen kare talakawa, kuma fitila ga miliyoyin mutane in ji shugaban Nijeriya Bola Tinubu

A cewar Tinubu, rasuwar Paparoma wadda ta biyo bayan bikin Ista, wata alama ce ta da ke nuna cewa ya koma ga Mahaliccinsa a wani lokaci da Kiristoci ke cike da sabuwar fata da bege.

Google search engine

Ya ce a cikin 2013, da ya zama shugaba a duniya Paparoma Francis ya yi hidima ga mabiya addinin kirsta da ke fadin duniya ta re da kira ga shugabanni da su yi adalci ga al’umma su tare da kokarin hade kan al’umma wajen rungumar zaman lafiya.

Ya kara da cewa Paparoma ya tsaya tsayin daka ga kasashe masu tasowa, inda ya dunga magana kan rashin adalci tare da yin addu’ar zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankunan da ke fama da rikici a fadin duniya.

Tinubu ya ce rashin Paparoma Francis ya sa duniya ta rasa mafi girma wajen kira a yi adalci tare da neman zaman lafiya ga al’umma baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

‘Yan majalisar dokoki 6 a Jihar Zamfara sun fice daga PDP zuwa APC

‘Yan Majalisar Dokokin Jihar Zamfara 6 da aka zaɓa a ƙarƙashin jam’iyyar PDP sun sauya sheƙa zuwa jam’iyya mai mulki ta APC, suna zargin take...

Kotu ta umurci hukumar EFCC ta gabatar da kwamshinan kudi na jihar Bauchi ga kotu bisa zargin safarar N4.6bn

Kotun Tarayya da ke Abuja ta umurci Hukumar EFCC da ta gabatar da Kwamishinan Kuɗin Jihar Bauchi, Yakubu Adamu, a ranar 30 ga Disamba domin...

Mafi Shahara