![]() |
| Jihar Rivers |
Wata babbar kotu a jihar Rivers ta bawa gwamnatin jihar umarnin cewa ta biya diyyar Naira biliyan 1 da miliyan 100 ga mutanen da aka rushewa kadarorinsu ba bisa ka’ida ba a Mile One da Mile Two da ke karamar hukumar Fatakwal.
Da yake yanke hukunci a Larabar nan mai shari’a Sika Aprioku, yace gwamnatin ba ta sanar da al’ummar da abin ya shafa ba kafin ta yi rusau din, inda ya ce, kotun ta samu gwamnati da laifin kwace musu filayensu da karfi.
Tun a shekarar 2022 ne dai, mazauna jihar da abin ya shafa, suka shigar gwamnatin kara gaban kotu bisa zargin tauye hakkokinsu.




