DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Mun ji takaicin ficewar gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta daga PDP zuwa APC- Umar Damagum

-

Shugaban ruko na jam’iyyar PDP na ƙasa, Umar Damagum, ya bayyana ficewar Gwamna Sheriff Oborevwori na Jihar Delta, tare da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar zuwa jam’iyyar APC, a matsayin abin takaici da kuma raɗaɗi.

Damagum ya bayyana haka ne a wani biki da aka gudanar a Abuja domin mika takardar shaidar nasara ga Jude Ezenwafor, wanda jam’iyyar PDP ta tsayar a matsayin ɗan takarar gwamna a Zaben jihar Anambra dake tafe, inda yace shugabancin jam’iyyar na PDP yana yin nazari domin kafa kwamitin rikon ƙwarya a jihar Delta.

Google search engine

Damagum ya ce babban zaɓen shekarar 2027 ba zai ta’allaka ga yawan gwamnoni da kowace jam’iyya ke da su ba, ya kuma yi kira ga dukkan ‘ya’yan jam’iyyar da su ɗaure damara, su haɗa kai domin ceton Najeriya, yana mai jaddada cewa babu wani ƙalubale da ba za su tunkara ba.

Gwamna Oborevwori da wanda ya gaji, tsohon Gwamna Ifeanyi Okowa, tare da wasu jiga-jigan PDP a jihar, sun sauya sheƙa zuwa APC a ranar Laraba, lamarin da ya kawo ƙarshen jita-jitar da ta dade tana yawo a jihar.

Tun daga farkon mulkin dimokuraɗiyya a shekarar 1999, jam’iyyar PDP ce ke jan ragamar mulki a jihar ta Delta dake da arzikin man fetur a shiyyar kudu maso kudancin Najeriya.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttp://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Babban Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Majalisar dattawa ta bukaci a dauki matasa aikin tsaro domin magance matsalar tsaro

Majalisar dattawan Nijeriya, ta nuna damuwa kan tabarbarewar tsaro a ƙasar, tana kira ga shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya amince da daukar matasa akalla...

Matukar dimokradiyya ta gaza a Nijeriya sai ya shafi fadin Yammacin Afrika – ECOWAS

Kungiyar tattalin arzikin kasashen Yammacin Afrika, ECOWAS, ta gargadi cewa duk wani rauni da dimokuradiyya ta samu a Nijeriya zai yi sanadin rushewar tsarin a...

Mafi Shahara