Bankin Duniya ya bayyana cewa yawan mutanen Najeriya da ke fama da talauci zai karu nan da shekarar 2027, duk da kasancewar kasar na daga cikin kasashen da Allah ya hore da albarkatun kasa.
Wannan na cikin rahoton Africa Pulse da aka fitar yayin taron asusun bada lamuni na duniya IMF da Bankin Duniya da ke gudana a birnin Washington D.C na Amurka.
Rahoton ya nuna cewa yankin Afrika ta Kudu da kasashen yankin Sahel (Sub-Saharan Africa) na da mafi yawan talakawa a duniya, inda kusan kaso 80 cikin 100 na talakawan duniya ke zaune a wannan yanki.
Najeriya na daga cikin kasashe hudu da ke dauke da rabin yawan talakawan da suka kai miliyan 560 a Afrika.