Jami’an rundunar ‘yan sandan Nijeriya sun dakile wani yunkurin yin garkuwa da mutane a hanyar Funtua zuwa Gusau a Katsina.
Jami’an sun yi artabu da ‘yan bindigar da ke dauke da muggan makamai, lamarin da ya tilasta musu tserewa da raunukan harbin bindiga.
A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, Muyiwa Adejobi ya fitar a ranar Lahadi, ta ce jami’an sun yi nasarar dakile yunkurin dauke mutane goma da direbobi biyu da fasinjoji takwas – ba tare da sun ji rauni ba kuma suka koma ga iyalansu.