DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Muna kokarin bunkasa tattalin arzikin Nijeriya zuwa dala tiriliyan 1 – Kashim Shettima

-

Mataimakin shugaban Nijeriya Kashim Shettima ya ce gwamnatin kasar na kan hanyar bunkasa tattalin arzikin Nijeriya zuwa dala tiriliyan 1 cikin shekaru goma masu zuwa.

Kashim Shettima ya ce don cimma wannan buri ana da bukatar haɗin gwiwa da ƙwararrun da za su iya jagorantar lamarin.

Google search engine

Ya yi wannan magana ne a birnin Legas a yayin taron da Africa and Middle Depositors Association (AMEDA) da Central Securities Clearing System (CSCS) Plc ne suka shirya.

A jawabinsa, Shettima ya jaddada kudirin gwamnatin na karfafa tsarin hada-hadar kudi a Nijeriya ta hanyar bin tsari da gyara dabarun bunkasa kasuwannin, da kuma hadakar gwamnati da masu masana’antu masu zaman kansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Gwamnonin PDP hudu sun isa Ibadan don gudanar da babban taron jam’iyyar

Gwamnonin PDP huɗu sun isa birnin Ibadan domin halartar babban taron kasa da jam’iyyar ta shirya, duk da hukuncin kotun tarayya da ta bayar na...

Likitoci sama da 4,000 sun bar Nijeriya a 2024 – Rahoto

Wani rahoto ya nuna cewa likitoci 4,193 ne suka fice daga Nijeriya don neman rayuwa mai inganci a shekarar 2024. Labari mai alaka: Likita daya na duba...

Mafi Shahara